Jirgin kasan daya taso daga Abuja zuwa Kaduna ya kashe kananan yaran wanda tagwayene mata a karamar hukumar Tafa.
Lamarin ya farune da misalin karfe 10 na safe ranar Asabar, kamar yanda jaridar The Cable ta ruwaito.
Yaran, Hassana and Hussaina Baro shekarar su daya da watanni 6.
Kakakin ‘yansandan jihar Naija, Wasiu Abiodun ya tabbatar da daruwar lamarin.
Yace yaran suna wasa ne akan titin jirgin kasan kamin lamarin ya faru.