Friday, August 28
Shadow

Jirgin kasa dake jigila tsakanin Kaduna zuwa Abuja ya taka tare da kashe yara mata tagwaye a jihar Naija

Jirgin kasan daya taso daga Abuja zuwa Kaduna ya kashe kananan yaran wanda tagwayene mata a karamar hukumar Tafa.

Lamarin ya farune da misalin karfe 10 na safe ranar Asabar, kamar yanda jaridar The Cable ta ruwaito.

Yaran, Hassana and Hussaina Baro shekarar su daya da watanni 6.

Kakakin ‘yansandan jihar Naija, Wasiu Abiodun ya tabbatar da daruwar lamarin.

Yace yaran suna wasa ne akan titin jirgin kasan kamin lamarin ya faru.

Karanta Wannan  Bayani Dalla-Dalla: Kan halin da ake ciki tsakanin Najeriya da kasar Amurka, bayan da shugaba Tinubu ya shafawa fuskarsa toka yace Najeriya ba zata yadda a kawo matsa gagararru ba wanda suka gagari Amurka da kasarsu ta Venezuela ba

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *