Tuesday, August 25
Shadow

JUNE 12: “Ku kira ni da duk sunan da kuke so,” Inji Tinubu, yana alƙawarin kare yancin faɗin albarkacin baki

Shugaba Bola Tinubu a ranar Alhamis ya yi alkawarin kare haƙƙin dimokuraɗiyya na ‘yan Najeriya na ‘yancin faɗar albarkacin baki.

A cikin jawabin Ranar Dimokuraɗiyya da ya gabatar a Majalisar Tarayya da ke Abuja, Shugaban ya ce wa jami’an tsaro kada su tsananta wa waɗanda ke sukar manufofin gwamnatinsa da ake ganin ba su yi wa jama’a daɗi ba.

“Dimokuraɗiyya na buƙatar haƙuri da kalamai masu zafi da cin mutunci,” in ji Tinubu a gaban ‘yan majalisa daga Majalisar Dattawa da ta Wakilai.

“Ku kira ni da duk sunan da kuke so, ku faɗi abin da kuke so, amma ni zan ci gaba da kira ga dimokuraɗiyya ta kare haƙƙinku na yin hakan.”

Karanta Wannan  YANZU YANZU: An Binciko yadda Nuhu Ribaɗu yayi Awun gaba da wasu Biliyoyin kuɗaɗe a lokacin da yake shugaban Hukumar EFCC, inji Fitaccen mai Binciken nan Dr. Idris

Tinubu ya shawarci magoya bayansa da ‘yan majalisa su fifita tattaunawa fiye da mulkin danniya, su fifita shawo kan juna fiye da tilastawa, da kuma kare haƙƙoƙin jama’a fiye da amfani da ƙarfi.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *