Wednesday, January 15
Shadow

Kalaman yabo ga masoyiyata

Kece tawa wadda ba zan bari kowa ya taba min ke ba.

Ina sonki fiye da yanda kike tunani.

Ke kyakkyawace ga kwarjini.

Idan kika yi murmushi ji nake kamar shokin din wutar lantarki ya kamani.

Babu wanda zai rabani dake ba zan taba yadda ba.

Idanunki farare kamar farin wata.

Shin wai meke faruwane, kullun idan na ganki sai inga kina kara kyau.

Hakoranki fari tas babu datti kamar Alli.

Gaki da dogon hanci kamar biro.

Ke ba balarabiya ba amma kinfi larabawa gwarjini.

Ke ba baturiya ba amma kinfi turawa kyan diri.

Ke ba ‘yar Indiya ba amma kinfi matan indiya zubi.

Karanta Wannan  Shagwaba a soyayya

Dirinki kamar na kwalbar lemun koka kola ko kuma ince kalangu.

Diddigenki daf-daf be yi fadi ba kuma bai yi kankanta ba.

Fatarki kullun sheki take kamar madubi.

Fuskarki tana matukar burgeni sosai.

Ina sonki kamar in yi hauka.

Kin sace zuciyata a lokaci guda.

Yatsun hannunki suna burgeni sai inji kamar inta sudesu kullun.

Ina sonki ba da misali ba.

Kina min kwarjini kamar zaki.

Kin iya kwalliya, ko dawisu Albarka.

Tafiyarki na sakani a wani yanayi na shauki.

Ina son in kasance tare dake ko dan in ta kallon murmushinki.

Kina da kyau ko baki sa hoda ba.

Ina son samun damar dandana yawunki.

Karanta Wannan  Kalaman soyayya zuwa ga saurayi

Abokaina na ta mamakin irin son da nake miki, amma ba zasu gane ba, ya zama kauna kuma kin mallake komai nawa.

Kece farin cikin zuciyata a ko da yaushe.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *