Friday, December 5
Shadow

Kalli Bidiyo: Mutane basa yawo shiyasa suke mamaki dan nace an bani kwangilar Biliyan 4 suna ganin karyane, Ni kuma ina yawo, ba kasuwancin da bana yi kuma yanzu haka an sake bani gidajen Naira Biliyan 5 in sayar>>Mansurah Isa

Tauraruwar fina-finan Hausa, Mansurah Isah ta bayyana cewa, mutane na mamakin tace an bata kwangilar Naira Biliyan 4.

Tace abinda da yawa basu fahimta ba shine, ba wai Biliyan 4 tsabar kudi ake magana ba, ana maganar a rubucene.

Tace idan tsabar kudi ake magana, ko Dangote da me kudin Duniya, Elon Musk basu taba ganin Biliyan 4 a zahiri ba duk yawanci a takarda ne.

Tace kuma matsalar mutane basa yawo ne shiyasa, tace amma ita tana yawo kuma ita ‘yar kasuwa ce dan haka ko a yanzu ma an bata gidajen Naira Biliyan 5 ta sayar a Abuja.

Karanta Wannan  Mutane 171 sun mutu bayan hadarin jirgin sama

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *