Kungiyar ‘yan uwa musulmi da aka fi sani da shi’a aun koka kan cirewa matansu Hijabi da ‘yansanda suka yi a Abuja.
Kungiyar tace wannan cin zarafine da kuma batanci ga addinin musulunci.
Wakiliyar mata ta kungiyar ‘yan uwa musulmi, Maryam Sani ta bayyana a wata sanarwa data fitar cewa zasu yadawa duniya wannan lamari a gani.
Kuma zasu kai maganar kotu.
Bidiyo dai ya bayyana a kafafen sada zumunta inda aka ga ‘yansanda na cirewa matan ‘yan shi’ar Hijabi ta karfin tsiya.