Saturday, March 21
Shadow

Kalli Bidiyon: A yi Hakuri, Abinda nake nufi shine ba zan baiwa wanda bashi da sana’a diyata ba>>Inji Ali Jita

Tauraron Mawakin Arewa, Ali Isa Jita ya bayyana cewa, abinda yake nufi shine ba zai baiwa wanda bashi da sana’a diyarsa ba.

Ya bayyana hakane a wani sabon Bidiyon daya wallafa bayan da Bidiyo na farko ya jawo cece-kuce inda aka rika ruwaito cewa yace ba zai baiwa Talaka diyarsa ba.

Jita yace ko Annabi(Sallallahu Alaihi Wasallam) ya nemi tsari daga Talauci.

Yace kumama menene zai sa mutum ya ji cewa wai dashi ake da zarar an ce Talaka?

Sannan yayi kira ga masu kafeshi shi da ‘ya’yansa mata cewa hakan bai dace ba su daina dan ya sabawa doka.

Karanta Wannan  Gwamna Abba Kabir Yusuf ya sakawa kasafin kudin 2026 hannu, saidai rashin mataimakin gwamna a wajan ya jawo cece-kuce

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *