
Tauraron Mawaki, Soja Boy ya bayyana cewa Addu’a bata karbuwa da addu’a tana karbuwa da matsalar Najeriya ta zo karshe.
Ya bayyana hakane a wani Bidiyo daya wallafa a shafinsa na Tiktok inda yace da Addu’a na aiki da kayi kudi, saboda tun yaushe kake rokon Allah ya baka kudi amma har yanzu baka yi kudin ba?
Soja Boy dai ya bayyana cewa aiki ake tashi a yi Tukuru kuma babu kasar data gyaru ta hanyar yin Addu’a.