
Amaryar Dan siyasa kuma dan kasuwar gidaje a Abuja, Saleem Goje me suna Hafsat Kamal ta masa tonon Asiri kan matan da yake soyayya dasu.
A cikin matan da take zargi akwai Tauraruwar fina-finan Hausa, Hadiza Gabon inda matar ta Saleem ta wallafa irin hirar da mijin nata ke yi ta WhatsApp da Hadiza Gaon.
A cikin Screenshot din data bayyana an ga inda Saleem yake cewa, yana son aikata Alfasha da Hadiza Gabon.

Sannan kuma an ga yanda ya aika wa gabon din da hotunan da basu kamata ba.
A wani screenshot din ma an ga cewa, hadda Azumi akwai lokacin da Hadizan Gabon din da Saleem Goje suka kasance tare.
Sannan itama Hadizar a wani screenshot din na daban, an ga yanda ta aikawa Saleem Goje da hotunan tsiraici.

Hakanan Hafsat Kamal watau matar Saleem Goje ta zargeshi da bin wata matar aure wadda itama suke soyayya.
Sannan ta zargi wasu da yi mata Sihiri suka hanata haihuwa.
Ta hau Live a Instagram tana ci gaba da kora bayani inda aka ga tana ta guje-guje a cikin gidan ta inda tace an turo mutane su je su kamata.
Ta rika fadar cewa, ga mutanen a kofarta suna shirin ballawa su je su kamata.
An dai ga mutane da yawa a kofar gidanta dake Abuja.
Mutane da yawa sun yi ta sharhi akan lamarin inda wasu ke ta mamakin yanda Hadiza Gabon ta shigo labarin.