
Me martaba sarkin Kano, Muhammad Sanusi II ya bayyana cewa, rashin adalcin da akewa abokinsa, tsohon Gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasiru Ahmad El-Rufai bai kamata ba.
Ya bayyana cewa, Sharudan belin da aka sakawa El-Rufai sun yi tsauri, yace kuma ba wai yana magana saboda malam Nasiru Ahmad El-Rufai bane.
Yace idan yau El-Rufai ake ma haka, gobe abin kan wani zai fada.