Sunday, August 9
Shadow

Kalli Bidiyon: Duk da DSS sun janye karar da suka shigar akan zargin Malam Nasiru Ahmad El-Rufai, kotu ta ki amincewa ta bayar da belinsa

A yau ne dai hukumar tsaron farin kaya ta DSS ta janye karar data shigar akan malam Nasiru Ahmad El-Rufai inda ta zargeshi da yiwa wayar babban me baiwa shugaban kasa shawara akan harkar tsaro, Malam Nuhu Ribadu kutse.

Bayan janye karar, Lauyoyin Malam Nasiru Ahmad El-Rufai sun roki kotu da cewa, ta taimaka ta rage sharudan bayar da belin malam Nasiru Ahmad El-Rufai saboda sun yi tsauri.

Lauyoyin na Malam Nasiru Ahmad El-Rufai sun bayyana cewa, sun yi iya bincikensu basu samo ma’aikacin gwamnati dake mataki na 17 dake da gida a Maitama ba.

Lauyoyin sun kara da cewa, dan haka suna neman a sassauta sharudan bayar da belin na Malam Nasiru.

Karanta Wannan  An kàshè mutum fiye da 1500 da sace fiye da 2000 a Najeriya - NHRC

Saidai kotun ta yi watsi da wannan bukatar tasu inda DSS suka sake tasa keyar Malam Nasiru Ahmad El-Rufai suka tafi dashi.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *