
Shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ya gana da Gwamnan kano, Abba Kabir Yusuf a fadarsa dake Abuja a yammacin ranar Litinin.
Ganawar tasu na zuwane yayin da ake ta rade-radin cewa, Gwamna Abba Kabir Yusuf zai koma jam’iyyar APC.
A sanarwar da me magana da yawun gwamnan, Sunusi Dawakin Tofa ya fitar, yace gwamna Abba ya gabatarwa da shugaba Tinubu tsare-tsaren gwamnatinsa ne da suka hada da samar da Tsaro, da Ayyukan ci gaba da kuma Hada kai da Gwamnatin tarayya.
A sanarwar da Shugaban jam’iyyar APC na jihar Kano, Abdullahi Abbas ya fitar, yace a yau, Talata ne Gwamna Abba Kabir Yusuf zai karbi katinsa na zama dan jam’iyyar APC.