Thursday, May 7
Shadow

Kalli Bidiyon ganawar da shugaba Tinubu yayi da Gwamnan Kano Abba Kabir Yusuf

Shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ya gana da Gwamnan kano, Abba Kabir Yusuf a fadarsa dake Abuja a yammacin ranar Litinin.

Ganawar tasu na zuwane yayin da ake ta rade-radin cewa, Gwamna Abba Kabir Yusuf zai koma jam’iyyar APC.

A sanarwar da me magana da yawun gwamnan, Sunusi Dawakin Tofa ya fitar, yace gwamna Abba ya gabatarwa da shugaba Tinubu tsare-tsaren gwamnatinsa ne da suka hada da samar da Tsaro, da Ayyukan ci gaba da kuma Hada kai da Gwamnatin tarayya.

A sanarwar da Shugaban jam’iyyar APC na jihar Kano, Abdullahi Abbas ya fitar, yace a yau, Talata ne Gwamna Abba Kabir Yusuf zai karbi katinsa na zama dan jam’iyyar APC.

Karanta Wannan  Bidiyon Dansandannan ya yadu sosai bayan da yace duk Sojan da ya ke ji shi kwallon Shyege ne ya je yawa 'yansandan Rundunar 'Police Special Forces' rashin kunya yaga yanda zata kare tsakaninsu
https://twitter.com/i/status/2013278927289012474

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *