Friday, January 16
Shadow

Kalli Bidiyon: Gwamnan jihar Kebbi tare da soja me guntulen Hannu da ya jawo cece-kuce sosai

A ranar Tunawa da ‘yan mazan jiya, Gwamnan jihar Kebbi, Nasiru Idris ya hadu da wani soja da ya rasa hannunsa a wajan aiki.

An gabatar da sojan a wajan gwamnan, inda gwamnan yace a yiwa sojan hannun Roba, inda yace a masa me kyau, har yana tambaya duka nawa yake?

Saidai wannan lamari ya jawo cece-kuce inda masu sharhi suka zargi gwamnan da rashin nuna tausai ga sojan musamman ganin cewa ya rasa hannun nasa ne wajan yiwa kasa Hidima.

Karanta Wannan  NNPCL Ta Zaftare Farashin Man Fetur Daga Naira 910 Zuwa Naira 895

Masu Sharhin na ganin cewa ba maganar kudi kawai bace, ya kamata gwamnan ya nuna alhini da halin da sojan ke ciki.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *