
Tsohon Ministan sufuri, Rotimi Amaechi ya bayyana cewa, Idan ya samu Mulki, Satar da zai yi ba zata wuce kaso 20 cikin 100 ba.
Ya bayyana cewa dalilin da yasa yace haka shine, bawai zai saci kudin mutane bane, amma idan ka samu mulki akwai abubuwan da darajar da kujerar da mutum yake kai take jawo masa.
Yace misali akwai bashin da idan ba kana kan mulki ba, ba zaka iya ci ba, hakanan akwai misali wani aiki da aka taba yi lokacin yana Gwamnan jihar Rivers wanda aka ce ya dauki kaso 10 na aikin a matsayin ladarsa wanda Biliyoyin Naira ne.
Yace dan haka bawai sata kai tsaye yake nufi ba.