Sunday, August 9
Shadow

Kalli Bidiyon: Irin wulakancin da akawa ‘yan kwallon kasar Senegal a kasar Amurka, an rika musu bincike kamar wasu rikakkun masu laifi

A wani Bidiyo da ya watsu a kafafen sada zumunta an ga irin binciken da akewa tawagar ‘yan kwallon kasar Senegal a dilin jirgin kasar Amirka.

‘Yan kwallon da suka je buga wasan gasar cin kofin Duniya ta World Cup an gansu ana musu bincike na kwakwaf wanda ya jawo Allah wadai.

A lokaci guda kuma an ga irin tarbar karamci da akawa ‘yan kwallon kasar Mexico.

Karanta Wannan  Kalli Bidiyo: Yanda wasu musulmai a kasar Amurka suka fito suna neman a Haramta Shan giya, Cin Nqmqn Alade da Caca

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *