
Dr. Rabiu Musa Kwankwaso ya bayyana cewa, suna magana da wata jam’iyya inda yace zai koma cikinta.
Yace amma ya saka musu sharadin sai in sun yadda zasu bashi takarar shugaban kasa ko ta mataimakin shugaban kasa.
Ya bayyana hakane a wajan taron da aka yi a gidansa na ‘yan Kwankwasiyya a Kano.
Saidai bai bayyana sunan jam’iyyar ba.
A baya dai, Hutudole ya ruwaito muku da Thisday cewa, jam’iyyar ADC ce Kwankwaso ke shirin komawa.