Friday, March 6
Shadow

Kalli Bidiyon: Labari me sanya Shauki, yanda wata mata data saba ciyar da karnuka, taje wajan Biki amma tasa aka kawo musu abinci

Wata mata a kasar India da ta saba ciyar da wasu karnuka kullun da dare.

Wata rana ta je wajan biki bata dawo ba sai ta sayi abinci, irin wanda ake kaiwa mutum har gida a mota ko a mashin.

Da dan sakon ya je kofar gidanta sai ya kirata yace ga abincin an kawo, sai tace bata nan.

Sai yace a ina zai ajiye?

Sai tace masa ya duba kusa da gidanta akwai wasu karnuka ya basu abincin , ta saba basu ne kuma tasan suna nan suna jiranta amma yau bata nan shiyasa tasa a kawo musu.

Haka dan sakon ya nemi karnikan ya basu abincin inda ya dauki Bidiyon lamarin saboda shima abin ya burgeshi.

Karanta Wannan  Kalli Bidiyon: Ni da ku Shyègyè ka fasa, zan zake siyo Motocin dakon ma fetur dan karya farashin man>>Dangote ya gayawa 'yan kasuwa masu shigo da man fetur daga kasar waje

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *