Bayan dawowar wutar lantarki a jihar Kaduna, Matasa sun hau titi inda suka rika wakar cewa Nepa ta dawo.
Bidiyon hakan ya watsu sosai a kafafen sada zumunta:
Wasu sun bayyana abin da Nishadi inda wasu kuma suka bayyana takaici da cewa ‘yan Kaduna sun bayar da kunya da wannan murna.
Kusan sati biyu aka kwashe ana fama da rashin wuta a yankin Arewa kamin a samu ta dawo.