
Tauraruwar fina-finan Hausa, Samha M. Inuwa ta fito ta bayar da hakuri kan Bidiyon ta da aka gani yana ta yawo a kafafen sada zumunta.
An dai ga wani Bidiyon ta inda aka ga tana share majina da takardar kudin Naira.
Bidiyon ya dauki hankula sosai inda akai ta sharhi akai mutane na bayyana mabanbanta ra’ayoyi
Saidai a nata jawabin tace wannan tsohon Bidiyon ne wanda ya kai kusan shekaru 4.
Tace kuma ko da a wancan lokacin, tana dora Bidiyon aka kirata aka gaya mata bai dace ba kuma ta hau ta cireshi.
Saidai tace har ofishin ‘yansanda aka gayyace ta a wancan lokacin kuma an rufe case din.