Tuesday, February 3
Shadow

Kalli Bidiyon: Tun shekarar farko ta Mulki Abba suka fara samun matsala da Kwankwaso>>Inji Sanat Rufai Hanga

Sanata Rufai Hanga ya bayyana cewa rashin jituwar dake tsakanin Gwamna Abba Kabir Yusuf da Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ta fara ne tun shekarar farko da fara Mulkin Abba.

Yace a wancan lokacin Sanata Kwankwaso ya so ganin Abba amma Abban yaki zuwa shi kuma idan ya ce zai je wajan Abban sai Abban yaki yadda ya ganshi.

Yace Sanata Kwankwaso ya gaya masa cewa, Lamarin ya dameshi saboda yanda yake ganin dansa Mustapha haka yake kallon Abba inda yace yana tunanin wani abu akawa Abba dan wannan ba Abban da ya sani bane.

Sanata Rufai yace Kwankwaso ya nemi a saka Gwamna Abba a addu’a inda daga baya suka samu ganawa.

Karanta Wannan  Kalli Bidiyo: Idan na auri ragon Namiji wanda bai iya biyamin Bukata Nasan Wuta zai kai ni dan Wallahi maza zan rika bi>>Murja Kunya

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *