
Tauraron Tiktok, Gfresh Al-amin ya baiwa ‘yan Tiktok dake zaune a Kano shawarar su bar garin.
Ya bayyana hakane a Bidiyon daya wallafa bayan sanar da shirin auren Maiwushirya da ‘YarGuda.
Gfresh yace An fara yiwa maza auren dole inda yace ko ba zasu iya kama gida a Abuja ba ko Kadunane su koma da zama ya fiye musu.