
A yau ne aka samu rahotannin dake cewa, tsohon gwamnan Kano, Dr. Rabiu Musa Kwankwaso ya kai ziyara fadar shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu.
Hakan na zuwane kwanaki kadan bayan da Tinubu ya kai ziyarar gaisuwar Aminu Dantata a Kano.
Da yawa dai nawa kallon ziyarar ta Kwankwaso a matsayin siyasa inda ake tsammanin zai iya komawa jam’iyyar APC.
Zuwa yanzu dai babu bayanai kan abinda suka tattauna.