
Dan majalisar tarayya karkashin jam’iyyar ADC, Leke Abejide ya bayyana cewa ba zasu bar jam’iyyar su a hannun baki ba da suka musu kaka gida ba.
Yace zai hada kai da ‘yan Asalin jam’iyyar ADC din dan su kwato jam’iyyar daga hannun wanda suka musu kaka gida.
Hakan na zuwane kwana daya bayan da tsohon mataimakin shugaban jam’iyyar na kasa, Nafiu Bala daga jihar Gombe ya bayyana kansa a matsayin sabon shugaban jam’iyyar na kasa na riko.
A wani labarin me kama da wannan, Gwamnan jihar Osun, Ademola Adeleke ya bayyana cewa ba zai koma jam’iyyar ADC ba.