Wani kamfani na kasar Japan me suna Obayashi Corporation wanda shine ya gina gini mafi tsawo a kasar na shirin gina Lifter wadda zata rika kai mutane wajen Duniyar mu dan su ga yanda lamura ke gudana.
Kamfanin yace zai fara wannan gini ne a shekara me zuwa watau 2025 wanda ake tsammanin kammalashi a shekarar 2050.
Wannan lamari dai ya zowa mutane da mamaki amma wanda yace zai hadiye kota sai a sakar masa a gani.