Friday, December 5
Shadow

Kaso 80 na ‘yan Najeriya sun ce basu yadda da gaskiyar shugaba Tinubu ba

Kaso 83 na ‘yan Najeriya sun ce basu amince da shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ba, kuma basu yadda da gaskiyarsa ba.

Wannan ya bayyana ne a sakamakon wata kuri’ar jin ra’ayin jama’a da wata kungiya me suna API ta shirya.

A kalla mutane 5,465 ne aka tambaya dake da shekaru 15 zuwa sama.

An gudanar da kuri’ar jin ra’ayin jama’ar ne da yarukan Pidgin, Hausa, Igbo, and Yoruba

Hakanan ‘yan Najeriya dai sun ce basu amince da bangaren shari’a ba.

An alakanta hakan da matsin tattalin arziki da ‘yan Najeriya ke fama dashi.

Karanta Wannan  Ko da 'yan Arewa basu yi Tinubu ba zai ci zaben 2027, saboda duka kudanci shi zasu zaba, kuri'a kadan yake nema daga Arewa ya ci zabe>>Inji Ayodele Fayose

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *