Friday, June 26
Shadow

Ke Uwace, Ki yi hakuri da rashin Kunyar da matan jihar mu suka miki, daukar nauyinsu aka yi>>Wike ya baiwa matar shugaban kasa, Remi Tinubu hakuri bayan matan jihar Rivers sun tashi sun fice daga dakin taro yayin da take jawabi

Ministan babban birnin tarayya Abuja, Nyesom Wike ya baiwa matar shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu watau Remi Tinubu hakuri kan abinda matan jihar Rivers suka mata.

A jiya Juma’a ne dai hutudole ya kawo muku rahoton cewa, matan jihar ta Rivers ana tsaka da taro sun tashi sun tafi yayin da matar shugaban kasar ke tsaka da jawabi inda suka ce basa son saurarenta.

Wike ta bakin kakakinsa, Lere Olayinka ya bayyana cewa wannan abin kunyane kuma daukar nauyin matan aka yi.

Yace wanda ke cewa yana neman sulhu ne wai yake irin wannan abin inda yace ba da gaske yake ba.

Karanta Wannan  Tsohon Gwamnan jihar Kogi, Yahya Bello da EFCC ke bincike kan zargin Satar Naira Biliyan 80 yace shugaba Tinubu ba sai ya je jikar Kogi yakin neman zabe ba, ya ci zaben 2027 a jihar

Wike yace a madadin al’ummar jihar Rivers kuma a matsayinsa na dattijo daga jihar Rivers yana baiwa matar shugaban kasar Hakuri.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *