
Wata matashiya dake shirin yin tafiya daga Damaturu zuwa Zamfara ta bayyana cewa, ‘yan Bindiga ko sun dauketa su sani ba’a damu da ita a gidansu ba.
Ta bayyana cewa babansu bai san iya yawan ‘ya’yansa ba hakanan itace ta 13 a wajan mahaifiyarsu.
Tace dan haka idan suka dauketa suka ce a biyasu kudi babu wanda zai biyasu.
Kalaman nata sun dauki hankula sosai.