Thursday, April 16
Shadow

Kotu ta bukaci a nemo mata Tsohuwar ministar Jinkai, Sadiya Umar Farouk Ruwa a jallo, saboda ta ki zuwa kotu wajan da ake Shari’ar ta ta zarginta da satar dala Miliyan $1.3 da Naira Miliyan 746.6

A zaman kotun dake Abuja da aka yi a yau, Alhamis 16 ga watan Afrilu na ci gaba da shari’ar tsohuwar ministar Jinkai, Sadiya Umat Frouk.

Sadiya da dayan wanda ake zargin me suna Bashir Nura Alkali wanda shine babban sakatare a ma’aikatar basu samu halarta ba.

Na ukunsu, Sani Nafiu Mohammed ne kadai ya samu halartar zaman kotun.

Dan hakane kotun tace a kamosu duk inda suke.

Ana dai zarginsu ne da sama da fadi da wasu rarar kudade na dala Miliyan $1.3 wanda ya kamata a ce an mayar da kudaden asusun gwamnati amma sai suka saka a aljihunsu.

Sannan akwai wasu kudaden suma da suka kai Naira N746,574,303 da ake zarginsu da sacewa.

Karanta Wannan  Idan ke matar aurece, ki sani Mijinki ba zai taba yin kwàncìyàr aùrè fiye da sau daya dake ba a dare

Jimulla ana musu zarge-zarge guda 21.

Ita dai Sadiya ta bayyana cewa ta je neman lafiya ne kasar Saudiyya shiyasa aka jita shiru.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *