
Kotun majistare dake Ikeja a jihar Legas a ranar Alhamis ta yanke wa Odunayo Ebenezer mai shekara 20 hukuncin zama a kurkuku bisa laifin yi wa dan shekara biyar fyade.
Alkalin kotun Mrs O. O Kushanu bayan ta yi watsi da rokon sassauci da Odunayo ta yi ta ce za ta yi zaman kurkukun har sai kotun ta kammala yin shawarar da fannin dake gurfanar da masu aikata laifi irin haka
An gurfanar da Odunayo a kotun bisa laifin cin zarafin dan shekara biyar ta hanyar yi masa fyade.
Kushanu ta ce za a ci gaba da shari’a ranar 4 ga Satumba.
Dansandan daya shigar da karan Adegoke Ademigbuji ya ce Odunayo wace ke zama a lanba
4 layin Idofian dake Shagisha a Magodo ta aikata wannan laifi ranar 4 ga Yuni.
Ademigbuji ya ce mahaifin yaron na zama a gidan iyayen Odunayo yana aiki inda a nan ne idan yarinyar ta ya yaron mutumin dake musu aiki ta ci zarafinsu.
“Mahaifin yaron ya bayyana wa jami’an tsaron cewa ya ga azakarin dansa mai shekara biyar a mike inda cikin lalashi ya tambayi yaron sannan yaron ya bayyana masa cewa Odunayo ta kira shi cikin wani daki inda ta ce ya kwanta sannan ta hay kansa ta kwanta.
Jami’in tsaron ya ce laifin da Odunayo ta aikata ya saba wa sashe 137 da 263 na tsaron dokokin hukunta masu laifin ta shekarar 2015 na jihar Legas.
Premium times Hausa.