
Gwamnatin shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ta mika kokon bararta ga ‘yan Najeriya cewa su sake zabenta dan ta sami ta kammala gyaran da ta dauko na tattalin arziki.
Gwamnatin tace idan aka zabi wani shugaban kasa wanda ba tituba, za’a samu matsala dan kuwa zai zo ya dakatar da dukkanin ayyukan da shugaba Tinubun ya fara ne.
Ministan harkokin jiragen sama, Festus Keyamo ne ya bayyana haka a wata hira da aka yi dashi a gidan talabijin na channels TV.
Keyamo yace duk wani dan APC ko yana so ko bayaso ya kamata ya ajiye son zuciya ya yi aiki tukuru dan ganin shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ya sake darewa kan mulki.
Yace ta hakane kawai zai samu damar kammala ayyukan ci gaba da ya fara dan kuwa a baya an ga yanda idan aka zabi sabon shugaban kasa yake dakatar da ayyukan ci gaba na shugaban kasar da ya gada.