Thursday, February 26
Shadow

Ku daure ku sake zaben Tinubu a 2027 ko dan ya kammala ayyukan ci gaban da ya faro a Arewa>>Femi Gbajabiamila shugaban ma’aikatan fadar Tinubu ya roki ‘yan Arewa

Shugaban ma’aikatan fadar shugaban kasa, Femi Gbajabiamila ya roki ‘yan arewa da su sake zaben shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu a zaben 2027.

Yayi wannan rokone a yayin wani taro da ya shirya na tsaffin ‘yan majalisar tarayya a Abuja.

Ya bayyana cewa, Shugaba Tinubu Tinibu ba shugaban kudancin Najeriya bane kadai, shugaba ne na kowanne yanki.

Yace ko dan Tinubu ya kammala ayyukan ci gaban da ya ke yi a Arewa, ya kamata ace ‘yan Arewan su sake zabensa.

Karanta Wannan  An gano wata hanyar da 'yan ìndìgà ke amfani da ita dan samun màyàkà da yawa ta hanyar amfani da mata

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *