Wednesday, January 15
Shadow

Kuka a daren farko

Mafi yawanci bisa al’ada amare na kuka a daren farko da suka shiga dakin mijinsu bayan an daura aure.

Saidai basu kadai ne ke wannan kukan ba.

Da yawa ciki hadda iyayen amarya, uba da uwa dukan akan samu wadanda ke yin wannan kuka.

Yawanci iyaye kan yi kukane bayan an daura aure a lokacin da ake tafiya da amarya zuwa gidan mijinta tana musu bankwana ko kuma suka gama yi mata nasiha.

A daidai wannan lokaci hawaye yakan kwacewa iyayen amarya.

Saidai wasu ba’a ganin nasu, suna yin na zuci ne kawai, ko kuma sai dare yayi sun ga gurbin diyarsu anan ne hawaye ko kukan zuci zasu fara bayyana a fuskar iyaye.

Karanta Wannan  Nasiha ga masoyiyata

Ita kuwa amarya a mafi yawan lokuta tana fara kukanta ne a yayin da aka kamota za’a sakata cikin mota dan zuwa gidan miji daga gidansu.

Za’a tafi da ita tana kuka har zuwa gidan mijin.

Saidai wasu basa yi.

Wata zata kasance a zaune a gefen gado kanta lullube da mayafi har zuwa lokacin da ango zai shigo da abokansa, su gama yi musu nasiha.

Watan ba zata ce uffan ba har a gama wannan bayani na abokai.

Kukan amarya a daren farko wanda aka fi sani shine wanda take yi a lokacin jima’i.

Mafi yawanci nishi kawai zaka ji amarya na yi, a wasu lokutan kuma wata bata yi, amma a mafi yawan lokaci amare na yin wannan kuka na dan lokaci ba me tsawo ba.

Karanta Wannan  Allah Sarki: Ji yanda auren wata mata ya mutu saboda kissar kishiya

Kuma shima Ango idan yaga abin zai yi yawa yakan lallashi amaryarsa ya kyaleta ta huta.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *