Jam’iyyar PDP ta mayar da martani kan kalaman da sanata Rabi’u Kwankwaso, dan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar NNPP a zaɓen 2023 ya yi wanda ya yi iƙirarin cewa jam’iyyar PDP ba ta da wani tasiri a siyasar Najeriya, inda ya ce jam’iyyar ta mutu.
A ranar Asabar ne dai Sanata Kwankwaso yayin buɗe ofishin jam’iyyar NNPP na jihar Katsina, jagoran Kwankwasiyyar ya zargi jam’iyyar PDP da APC mai mulki da jefa kanta cikin abin da ya kira ”halaka”.
A cikin wata sanarwa da sakataren yaɗa labaran jam’iyyar na ƙasa Debo Ologunagba ya fitar a ranar Lahadi, PDP ta bayyana Kwankwaso a matsayin “mara muhimmanci a siyasar Najeriya” tare da zargin sa da son kai.
Ologunagba, ya soki kalaman Kwankwaso, inda ya nuna cewa jam’iyyar NNPP a karkashin shugabancin Kwankwaso na ƙoƙarin gina kanta ne a jiha ɗaya kacal, yayin da kuma jam’iyyar PDP har yanzu na da tasiri a faɗin jihohi 13 da ke da gagarumin wakilci a majalisar dokokin ƙasar.
Sanarwar ta ce “Rabi’u Kwankwaso ba shi da wani tasiri a siyasar Najeriya a yau idan aka yi la’akari da yadda yake fafutukar ganin ya jagoranci wata jam’iyya mai suna NNPP wadda ita ma ke fafutukar ganin ta gina kanta a jiha ɗaya kawai.”
“Abin da za a fi mayar da hankali a nan shi ne yadda Sanata Kwankwaso ya nuna tsananin son kai, wanda hakan ke nuna cewa shi ba shugaba ba ne.”
PDP ta ce abin mamaki ne yadda Kwankwaso, wanda suka bayyana a matsayin dan siyasar da ya gaza, zai ayyana jam’iyyar da ke da ƙasa baki daya a matsayin ta mutu.
PDP ta kara zargin Kwankwaso da fifita burinsa na siyasa fiye da jin dadin ‘yan Najeriya.
“Shugaba na gaskiya zai mayar da hankali ne wajen magance matsalolin da ke addabar ƙasar maimakon yin kalamai masu kawo raba kan jama’a.” sanarwar ta ƙara da cewa.
Da yake karin haske kan matsalar tattalin arzikin da ake fama da shi a halin yanzu, Ologunagba ya jaddada cewa ‘yan Najeriya na cikin mawuyacin hali a karkashin gwamnatin jam’iyyar All Progressives Congress (APC).
“Kwankwaso ya fi mayar da hankali kan burinsa na zama shugaban kasa yayin da ‘yan Najeriya ciki har da na jiharsa ta Kano ke fama da yunwa da ƙunci.”
“Sama da mutane miliyan 150 ne suka fada cikin talauci, inda miliyoyi suka rasa abin dogaro da kai, yayin da hauhawar farashin kayayyaki da man fetur suka yi tashin gwauron zabi.” in ji sanarwar.
PDP ta kara da cewa siyasar Kwankwaso ta samo asali ne tun lokacin da ya ke jam’iyyar, kuma abin takaici ne yadda ya ci gaba da mayar da hankali kan burinsa a irin wannan mawuyacin lokaci da kasar ke ciki.