
Shugaba Bola Tinubu ya amince da samar sa sabbin asibitocin sha-ka-tafi guda dubu 8,800 a fadin kasar nan da kuma inganta manyan asibitoci da ake da su don magance cutukan damuwa da cutuka masu yaɗuwa.
Mataimakin shugaban kasa, Sanata Kashim Shettima ne ya bayyana hakan a yau Asabar a lokacin da ya kaddamar da cibiyar kula da cutar damuwa ta Sulaiman Adebola Adegunwa a garin Sagamu na jihar Ogun.
Mataimakin shugaban kasar, a wajen taron, ya yi kira da a kara samar da asibitoci masu zaman kan su a wani ɓangare na sauye-sauyen da gwamnatin ke yi a fannin kiwon lafiya da ci gaban kiwon lafiya a fadin Najeriya.
Ya jaddada kudirin Gwamnatin Tarayya na magance matsalolin da ake fuskanta a fannin kiwon lafiya ta hanyar dabarun hadin gwiwa da zuba jari, yana mai cewa bude asibitoci masu zaman kansu suna da muhimmiyar rawa da za su taka domin “gwamnati ita kadai ba za ta iya sauke wannan nauyi ba.