Maganin rage kiba wanda bashi da illa a hankali ake samun sa, mafi yawan abubuwan rage kiba na dare daya suna illa sosai.
Ga hanyoyin da ake bu wajan rage kiba ba tare da shan magani ba:
A rage cin kayan zaki wanda basu da fiber.
A rage shan lemun kwalba, Biredi, cincin,biskit da sauransu, a yawaita cin Wake, Alkama, kwai, kifi da nama wanda bashi da illa.
A Motsa jiki:
Motsa jiki na da matukar muhimmanci idan ana son rage kiba. Ba wai sai mutum yayi abinda zai kure kansa ba, ko da tafiya da sauri-sauri ta isa, ana iya yinta na tsawon mintuna 30 zuwa 60 a kullun dan samun sakamako me kyau.
A daina cin abubuwan da kamfani ya sarrafa irin na leda kwalba da roba.
Anan ana maganar irinsu madarar gwagwani,Waken Gwangwani, Alewa, Biskit, da sauran duk wasu abubuwan da ba’a gida aka yi su ba.
Ka kasance tare da abokai ko dangi masu son rage kiba da kula da lafiyar jikinsu.
Rahoto ya bayyana cewa, Kasancewa tare da dangi ko abokai masu son rage kiba da kula da jikinsu na taimakawa sosai wajan kaima ka rage kiba.
Idan ana shan giya a daina:
Yawan shan giya na daya daga cikin hanyoyin dake sa mutum ya samu tumbi da yin kiba wadda ta wuce misali.
A rage shiga damuwa, saka kai cikin damuwa na daga cikin abubuwan dake karawa mutum tumbi da kiba.
A rage shan kayan zaki, a rika amfani da zuma ko dabino ko mazarkwaila,ko su din a rika amfani dasu saisa-saisa.
A rika yin usashshen bacci, rashin samun isashshen bacci na da alaka da yin Tumbi da kiba, a rika samun wadataccen isashshen bacci, musamman na dare.
A rika yin Azumi nan da can: Ko da a addini,akwai masu yin azumin litinin da Alhamis, to a likitance ma yin azumi nan da can yana da matukar amfani musamman ga masu son rage kiba da tumbi.