
Mahaifi me ‘ya’ya 11, Lawal Hamisu a jihar Kaduna, ya kai diyarsa me shekaru 27 kotun shari’ar Musulunci dake Magajin gari a jihar Kaduna.
Mahaifin ya nemi kotun ta cewa diyarsa ta fito da mijin aure.
Mahaifin ta bakin lauyansa, H.B Debo ya gayawa kotu cewa diyarsa shekarunta 27 kuma ta kammala karatun HND kuma tana kawo maza da yawa gida shine yake son ta fitar da mijin aure.
Yace so yake diyar tasa ta kaiwa kotu wanda take son aure, kotun ta daura musu aure tunda mahaifinsu ta bata masa suna a wajan ‘ya’yan nasa basa ganinsa da mutunci.
A jawabin diyar, tace bata da wanda yake son aurenta dan duk masu zuwa wajanta babu wanda ya nuna da gaske yake.
Mai shari’a, Malam Yakubu Abdullahi ya bayyana cewa, Wannan shari’ar nada muhimmanci kuma dan haka zai gana da su duka diyar da mahaifinta a asirce dan kawo karshen rikicin.
Ya daga shari’ar zuwa ranar 3 ga watan August dan yanke Hukunci.