
A jiyane, Dan tsohon Gwamnan Kaduna, Bashir El-Rufai ya bayyana cewa, Gwamna Uba Sani ya rika bin matan mahaifinsa yana rokonsu gwiwoyi kasa kan su roki mahaifinsa ya tsayar dashi takarar Gwamna.
Ya kara da cewa Gwamnan ya kuma rika bin na kusa da Mahaifinsa yana basu kudi dan suwa mahaifinsa magana ya tsayar dashi takarar.
Yace hakanan har yayan mahaifinsa ma saida Uba sani ya rika bi yana roko dan a tsayar dashi takarar Gwamna.
Saidai mahaifiyar Bashir, Hajiya Hadiza Ismail El-Rufai, ta karyatashi inda tace ba’a yi haka da ita ba.