Thursday, March 13
Shadow

Majalisar Dinkin Duniya ta saka Kasar Israela cikin masu kisan kananan yara

Majalisar Dinkin Duniya ta saka kasar Israela cikin kasashe masu kisan kananan yara.

Hakan ya biyo bayan kisan sa kasar kewa Falas-dinawa a zirin gaza.

Wakilin Israela a Majalisar Dinkin Duniya, Gilad Erdan ne ya bayyana haka. Inda yace an sanar dashi matakinne ranar Juma’a.

Hakanan ministan harkokin kasashen waje na kasar Israela, Katz ya bayyana cewa, zasu dauki mataki kuma wannan abu da majalisar ta yi zai canja dangantakar dake tsakaninsu da Israela.

Karanta Wannan  Ya kamata EFCC ta kyale Bobrisky ta koma kan 'yan siyasa>>Inji Peter Obi

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *