Saturday, December 13
Shadow

Majalisar Wakilai ta umarci a bada tsaro na tsawon shekaru 10 ga ɗan jaridar da ya bankado badakalar digiri dan kwatano

Majalisar Wakilai ta amince da bada kariya ta tsaro na tsawon shekaru 10 ga wakilin DAILY NIGERIAN mai binciken ƙwaƙwaf, Umar Audu, biyo bayan fallasa yadda ake baƙalar kwali digiri a Kwatano, amhuriyar Benin.

Binciken da Audu ya yi a boye ya bankado wani gungun mutane da ke taimaka wa ‘yan Najeriya siyan kwallon digiri da ba su yi karatun ba, wadanda da yawa aka sahale musu aiki a ma’aikatun gwamnati, ciki har da ma’aikatar ilimi suka wanke su ta hanyar damfara.

A halin yanzu dai kwamitin majalisar tarayya mai kula da jami’o’i, da fasaha, da harkokin cikin gida, da harkokin kasashen waje, da kuma ci gaban matasa, na binciken badakalar.

Karanta Wannan  Kalli Bidiyon: Abin takaici ne, mun gama Zhagin wadanda ba musulmai ba da cewa Arnane masu fitsari a tsaye amma yanzu munce Annabi(Sallallahu Alaihi Wasallam) shima yana fitsari a tsaye>>Inji Sheikh Nura Khalid

A zaman sa a yau Litinin, shugaban kwamitin, Abubakar Fulata, ya sanar da umarnin majalisar tare da yin kira ga rundunar ‘yan sandan Najeriya da sauran hukumomin tsaro da suka hada da hukumar tsaron fararen hula, NSCDC, da su tabbatar da tsaron Audu na tsawon shekaru goma masu zuwa.

“Muna godiya ga Audu bisa jajircewarsa, muna rokon ministan harkokin cikin gida da ya tabbatar da cewa jami’an tsaron NSCDC sun bayar da kariya da ake bukata tare da ‘yan sanda,” inji Fulata.

A cikin shaidar da ya bayar a gaban kwamitin, Audu ya bayyana yadda ya samu digirin digirgir na jami’ar Jamhuriyar Benin ba tare da ya je ya shiga a ji an koya masa ba kuma ma’aikatar ilimi ta amince da shi a kan kudi N40,000.

Karanta Wannan  Kalli Bidiyo: Dan Jarida, Audu Bulama Bukarti na ta shan Yabo saboda kin yadda ya gaisa da mace a wajan bikin kammala karatunsa na PhD

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *