Wa kike so ko kake ka mallaka, Budurwace, Saurayine? Akwai hanyoyin Mallaka da Tumfafiya da ake amfani dasu.
Saidai ba kowa ya sansu ba kuma ba kowane yakewa aiki ba sai wanda yayi dace.
Amma menene ingancin Amfani da Tumfafiya wajan mallkar wani?
Maganar gaskiya itace wannan hanya bata da inganci,zai iya zama sihiri ne ko surkulle wanda zai iya yin aiki, zai kuma iya zama bai yi aiki ba.
Ana mallaka ne ta hanyar kyautatawa da mu’amala me kyau.
Koma wanene kike so ko kake ka mallaka, babbar hanyar da za’a bi shine kyautatawa.
Muna maganar Kyautatawa ta bangaren Kyauta, kalamai, da mu’amala.
Misali Idan Mijine:
Ki rika kyautata masa ta hanyar tsaftace kanki farko, ya zamana bakinki baya wari, jikinki baya wari, kayan jikinki tsaf-tsaf masu kama jiki da fiddo surar jikinki.
Kada ki rika mai tsawa wajan magana, ki rika sanyaya murya a yayin magana dashi, idan zai yiyu, ki rika zama kusa dashi ko kan cinyarsa yayin da kuke magana.
Ki rika tabbatar kina mai irin girkin da yake so.
Wajan Kwanciya, karki rika nuna masa kosawa, ko ki rika hanashi a yayin da ya nemi biyan bukata dake.
Idan yana cikin damuwa, ki rika kokarin kwantar masa da hankali.
Idan ya baki labarin wani abu da yayi, ki rika kokarin karfafa masa gwiwa, ka da ki zama me zarginsa akan kuskuren da yayi, ki zama me samar masa mafita akan inda yayi kuskure.
idan kuma Macece ko budurwa ake son mallaka, Kyauta na da matukar muhimmanci, ma’ana, kyautar kudi data kayan sayawa da abinci.
Kalamai ma na da matukar tasiri sosai.
Ka rika yabonta, kana gaya mata irin muhimmancin da take dashi a wajenka da irin rayuwar auren da kake fatan ku yi tare da sauransu.