Friday, May 30
Shadow

Manyan Arewa kudi aka basu suka siyar daku shiyasa suke gayawa shugaban kasa, Arewa ba korafi, Subul da baka ne aka yi a Katsina maganar ta fito fili amma dama can haka suke gayawa shugaban kasa, saboda an biyasu, Inji Sheikh Nura Khalid

Babban malamin Addinin Islama, Sheikh Nura Khalid wanda aka fi sani da Digital Imam ya bayyana cewa, Manyan Arewa kudi aka basu shiyasa basa iya fitowa su gayawa shugaban kasa gaskiya suke ce masa Arewa ba korafi.

Kalmar Arewa ba Korafi ta fito ne daga jihar Katsina wadda ke fama da matsalar ‘yan Bindiga a lokacin da shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ya kai ziyara jihar, an ga wani babban allo dauke da kalmar Katsina ba Korafi.

Lamarin ya jawo cece-kuce inda akai ta sukar musamman manyan masu mulki na Jihar, har sai da ta kai ga gwamnan jihar ya fito ya nesanta kansa da wannan allo.

Karanta Wannan  An saka dokar hana hana zirga-zirga a jihar Kaduna

Saidai Sheikh Nura Khalid ya bayyana cewa, Subul da baka ne aa yi amma haka suke gayawa shugaban kasar.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *