
Matar tsohon Gwamnan Kaduna, Hajiya Hadiza Ismail El-Rufai ta wallafa a shafinta cewa, ICPC sun dauke mata na’urar da take amfani da ita a banki.
Tace tana rantsuwa da Allah na’urar ba ta kutsen waya bace.
Ta bayyana cewa, cikin kayan da ICPC suka bayyana cewa sun dauka daga gidan Malam Nasiru Ahmad El-Rufai, sun manta su bayyana wannan na’urar tata.
ICPC dai sun bayyana wayoyi da kwamfutocin tafi da gidanka a matsayin abubuwan da suka gano a gidan malam Nasiru Ahmad El-Rufai.
A baya kuma sun zargi cewa, sun gani na’urar yiwa waya kutse.