Friday, December 5
Shadow

Muna nan akan Bakan mu duk wanda zai yi wa’azi a Jihar Naija sai ya yanki Lasisi duk malamin da ya ji ba zai iya hakan ba ya fita ya bar mana jiharmu>>Inji Gwamnan jihar Naija, Umar Bago

Gwamnan jihar Naija, Umar Bago ya jaddada aniyarsa ta cewa, sai malami ya yanki Lasisi a jihar kamin a barshi yayi wa’azi.

Yace ba zasu bari malami ya hau mumbari ya rika zagin gwamnati da duk wanda yaga dama ba ko ya kawo wata sabuwar akida ba.

Yace duk malamin da ya ga hakan bai masa ba, yana iya karawa gaba.

Karanta Wannan  Maganar Wike ya baiwa 'ya'yansa manyan filaye a Abuja: Atiku ne saboda kiyayya yake son batamin suna>>Inji Wike

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *