Wednesday, January 15
Shadow

Muna nan akan bakarmu na baiwa shugaba Tinubu shawarar ya ci gaba da kara kudin man fetur>>IMF

Hukumar bayar da lamuni ta Duniya tace bata canja ba, har yanzu tana nan akan bakanta cewa shugaba Tinubu ya cire tallafin man fetur dana dala.

Hukumar tace ta hakane ‘yan Najeriya zasu samu saukin rayuwa daga matsin tattalin arzikin da suke fama dashi.

Karin farashin man fetur dai yasa kayan masarufi sun tashi sama sosai inda talakawa ke cin abinci da kyar.

Lamarin ya jawowa gwamnati tofin Allah tsine tsakanin Talakawa.

Hakanan an sha zargin hukumar ta IMF da bankin Duniya da bayar da shawarwarin dake jefa kasashe da yawa cikin wahalar rayuwa.

Karanta Wannan  Kalli Bidiyon yanda matar mutuminnan na kasar Equatorial Guinea da yayi lalata da mata 400 ke rufe fuskarta dan Kunya

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *