
Shugaban bankin Afrika, AFDB, Dr Akinwumi Adesina ya bayyana cewa, lalacewar tattalin arzikin Najeriya a yanzu ya fi muni fiye da lokacin da aka baiwa Najeriya ‘yancin kai a shekarar 1960.
Ya bayyana hakanne a wajan wani taro da ya faru a Legas ranar Alhamis.
Yace Abinda ake cewa GDP per capital wanda shine ake auna ma’aunin tattalin arzikin kasa dashi a yanzu yana kan Dala $824 ne.
Yace a yayin da a lokacin da aka baiwa Najeriya ‘yancin kai a shekarar 1960 GDP per Capital yana kan Dala $1,847 ne.
Yace hakan ba karamar matsala bace inda yace ya kamata Gwamnatin Najeriya ta tashi tsaye dan shawo kan wannan matsalar.