Friday, January 16
Shadow

Na ji dadin Fitowar Jam’iyyar ADC>>Inji Shugaban Ma’aikatan Fadar shugaba Tinubu, Femi Gbajabiamila, Ji dalilinsa

ADC: Gamaiyar am’iyyun adawa abu ne mai kyau da zai kare Najeriya daga mulkin jam’iyya ɗaya tilo– Gbajabiamila.

{“remix_data”:[],”remix_entry_point”:”challenges”,”source_tags”:[“local”],”origin”:”unknown”,”total_draw_time”:0,”total_draw_actions”:0,”layers_used”:0,”brushes_used”:0,”photos_added”:0,”total_editor_actions”:{},”tools_used”:{“square_fit”:1},”is_sticker”:false,”edited_since_last_sticker_save”:true,”containsFTESticker”:false}

Shugaban Ma’aikatan Fadar Shugaban Ƙasa, Femi Gbajabiamila, ya bayyana cewa haɗin gwiwar jam’iyyun adawa tare da amincewa da jam’iyyar ADC a matsayin jam’iyyar su na kalubalantar jam’iyya mai mulki babban ci gaba ne da zai taimaka wajen ƙarfafa dimokuraɗiyya a ƙasar.

Gbajabiamila ya bayyana haka ne a ranar Asabar yayin da yake zantawa da manema labarai bayan kada ƙurarsa a rumfar zaɓe ta PU 014 dake makarantar Elizabeth Fowler Memorial High School a unguwar Adeniran Ogunsanya, Surulere, yayin zaɓen ƙananan hukumomi a jihar Legas.

Ya ce: “Wannan wani ci gaba ne mai kyau tare da haɗin ƙawancen. Ba sabon abu bane muna ganin haka. Duk wata dimokuraɗiyya tana buƙatar samun adawa a wani mataki, in ba haka ba ƙasar za ta iya shiga mulkin jam’iyya ɗaya. Amma ban tabbata inda wannan zai kai mu ba.”

Karanta Wannan  Gwamnati ta shiga tsakani a rikicin Dangote da 'yan kasuwar man fetur da suke zargin Dangoten da yin kaka gida a harkar man fetur

A farkon wannan watan, jagororin ƙawancen jam’iyyun adawa sun taru a Cibiyar Yar’Adua dake Abuja, inda suka bayyana hukuncin ɗaukar ADC a matsayin jam’iyyar su na kalubalantar APC a babban zaɓen shekarar 2027.

A wajen taron, shugaban jam’iyyar ADC, Ralph Nwosu, ya mika katin membobinsu ga tsohon Shugaban Majalisar Dattawa, David Mark, da tsohon Gwamnan Osun, Rauf Aregbesola, waɗanda aka gabatar a matsayin shugaban rikon kwarya na jam’iyyar da kuma sakataren jam’iyya na ƙasa.

Fitattun ’yan siyasa da suka halarci taron sun haɗa da tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa, Atiku Abubakar; ɗan takarar jam’iyyar Labour Party a 2023, Peter Obi; tsoffin gwamnoni Nasir El-Rufai da Rotimi Amaechi; da sauran manyan ’yan siyasa kamar Dino Melaye, Dele Momodu, Solomon Dalung, Sanata Gabriel Suswam, Sanata Ireti Kingibe, Emeka Ihedioha, da Air Marshal mai ritaya Sadique Abubakar.

Karanta Wannan  SUBHANULLAH: Yanzu-Yanzu wata Motar Sumfuri ta gwamnatin jihar Sokoto ta samu mummunan hatsari a garin Zariya

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *