
Ministan babban birnin tarayya, Abuja ya gyara babban dakin taro na kasa da kasa dake Abuja wanda ya sakawa sunan Shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu.
Lamarin ya jawo cece-kuce inda masu suka ke cewa, a zamanin tsohon shugaban kasa janar IBB ne aka gina dakin kuma sunansa ya kamata a saka.
Saidai wani abu da ya kara daukar hankula shine maganar kudin da aka kashe wajan gyaran inda Ministan yace sun kashe Naira Biliyan 39 wajan yin wannan gyara.
Masu bin diddigi sun ce Naira Biliyan 39 dinnan zata iya gina Asibitoci 312 da Ajujuwan Karatu 1,200.
Hakan dai na nuna rashin muhimmanci da shuwagabanni basu baia bukatar talakawa, ko kuma ace rashin saka kudi inda aka fi bukatarsu.