Tuesday, March 25
Shadow

Najeriya ta ƙara yawan man da take haƙowa – Rahoto

Najeriya ta ƙara yawan man fetur da take haƙowa zuwa ganga 70,000 a kowace rana fiye da adadin da ƙungiyar OPEC ta sanya mata, kamar yadda nazarin kamfanin dillancin labarai na Reuters ya nuna.

A cewar nazarin, man da ƙasashe mambobin ƙungiyar OPEC – ta masu arzikin man fetur – su ka fitar a watan Fabrairu ya ƙaru, inda Iran ke kan gaba, duk da ƙoƙarin da Amurka ke yi na daƙile fitar da man.

Najeriya ta ƙara adadin man da take fitarwa da ya zarce adadin da ƙungiyar ta ware mata.

Ƙungiyar ta OPEC ta haƙo gangan miliyan 26 da 74,000 a kowace rana a watan da ya gabata, inda aka samu ƙarin ganga 170,000 a kullum idan aka kwantanta da watan Janairu, a cewar nazarin na Reuters.

Karanta Wannan  Kai da kace idan ka zama shugaban kasa zaka halasta shan Wìwì shine kake da bakin cewa musulmai Jahilai? Kaine babban dakiki>>Reno Omokri ya mayarwa Sowore martani

Ƙungiyar OPEC+ – wadda ta haɗa da ƙasashen OPEC da Rasha da sauran ƙawaye – na son rage yawan man da suke haƙowa a watan Maris sakamakon hasashen raguwar buƙatar man da kuma wayan fitar da man daga ƙasashen da ba sa cikin ƙungiyar.

To sai dai a ranar Litinin, ta yanke shawarar dakatar da shirin nata, inda take sa ran ƙara yawan man da take haƙowa a watan Afrilu.

Nazarin ya gano cewa ƙasar Iran ce kan gaba a wajen haƙo man, inda take haƙo ganga 80,000 a kowace rana, a cewar nazarin Reuters.

Fitar da ɗanyan mai daga Iran ya farfaɗo lokacin gwamnatin tsohon shugaban Amurka, Joe Biden duk da takuntuman Amurka, sai da ƙarkashin shugaba Donald Trump, Amurka na sabunta ƙoƙarinta na katse fitar da man baki-ɗaya.

Karanta Wannan  Zan Yi Tattaki Daga Jihar Gombe Zuwa Abuja Domin Kaiwa Maulana Prof. Ibrahim Maqari Ziyara, Inji Rumanatu Sa'ad Abubakar

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *