Monday, April 21
Shadow

Nijar ta ayyana Hausa a matsayin harshen da za’a rika amfani dashi a ƙasar

A Jamhuriyar Nijar gwamnatin kasar ta bayyana Hausa a matsayin harshen da za a rinka amfani da shi a kasar yayin da sauran harsuna ta ayyanasu a matsayin na magana.

Kazalika an kuma bayyana harshen Ingilishi da Faransanci a matsayin harsunan aiki.

To sai dai kuma ba dukkanin ‘yan kasar ne ke maraba da wannan mataki ba.

An kiyasta cewa akwai mutum miliyan 18 da ke jin harshen hausa a Jamhuriyar Nijar, abin da ake ganin wannan ne ya sanya gwamnatin kasar ta ayyana shi a matsayin harshen da za a rinka amfani da shi a kasar.

To sai dai kuma ba dukkanin ‘yan kasar ne wannan mataki ya yi wa dadi ba, inda wasu ke cewa ya kamata a yi nazari sosai a kai.

Karanta Wannan  Motocin dake kan titunan Najeriya sun rage saboda tsadar rayuwa da wahalar man fetur

Harshen Hausa shi ne ke matsayin na uku a Afirka inda kasashe da dama a Afirka a ke samun masu jin harshen.

Akwai dai masu jin harshen Hausa a kasashe kamar Najeriya da Nijar da Kamaru da Ghana da Chadi da Sudan da Benin da Togo da Gabon da kuma Burkina Faso.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *